EFCC ta janye daga neman kama Yahaya Bello
Janyewar na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban hukumar, ya sha alwashin sauka daga kujerarsa idan har ba a gurfanar da Yahaya Bello ba
Hukumar EFCC ta janye karar da ta daukaka a gaban kotu na neman kama tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello.
Lauyan EFCC, J.S Okutepa, SAN, ya shaida wa kotun da ke zama a Abuja cewa janyewar ta zama dole saboda sauyawar wasu abubuwa.
Janyewar na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban hukumar EFCC, Ola Olokoyede, ya sha alwashin sauka daga kujerarsa idan har ba a gurfanar da Yahaya Bello ba.
Aminiya ta ruwaito Olukoyede na zargin Yahaya Bello da biya wa dansa guda daya kudin makaranta Dala 720,000 daga asusun gwamanti a jajibirin saukarsa daga kujerar gwamnan Kogi, alhali lokacin biyan kudin bai yi ba.
- An kama malami kan lalata da ɗaliba a Jami’ar Nsukka
- Zan Yi Murabus Idan Ba A Gurfanar Da Yahaya Bello Ba —Shugaban EFCC
- Emefiele Ya Kashe N18.9bn Kan Buga Sabbin N684.5m —EFCC
Kafin janyewar, EFCC ta daukaka kara ne kan umarnin Babbar Kotu Jihar Kogi da ta hana hukumar kama tsohon gwamnan.
Hukumar ta ce ta mika wa kotu bukatar janye daukaka karar ce saboda lokacin da doka ta kayyade na yin hakan ya riga ya kure.
A ranar 8 ga Afrilu, 2024 Yahaya Bello ya shigar da karar neman kotu ta kare masa hakkokinsa na dan Adam, ta hana EFCC yi masa duk wata barazana ko kama shi ko aibata shi ba tare da ba shi takardar gayyata ta hanyar da ta dace ba.
Tsohon gwamnan ya kuma yi zargin cewa akwai wata manufar siyasa a shirin EFCC na kama shi ba bisa ka’ida ba.
Washegari kotun ta amince da bukatarsa ta hana EFCC “yi masa barazana ko kama shi ko wani jami’insa ko iyalinsa har sai alkali ya kammala shari’ar,” amma ta ce hukumar na iya kai karar shi idan akwai wani dalili na daban.
A ranar 12 ga Maris EFCC ta daukaka kara a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, bisa hujjar cewa kotun farko ba ta da hurumin hana hukumar gudanar da aikinta.
A ranar ce jami’an hukumar suka yi wa gidan tsohon gwamnan da ke Abuja kawanya domin kama shi, bayan sun samu izinin yin hakan daga kotun Abuja.
Sai dai kuma a karshe ba iya kama shi, bayan takaddamar da aka samu tsakanin jami’an hukumar da ayarin gwamnan Kogi mai ci, Usman Adodo wanda ya je gidan.
Hukumar na zargin Adodo da daukewa da kuma tserewa da Yahaya Bello daga gidan, amma gwamnan ya ce zargin ba shi da tushe.
EFCC na zargin Bello da laifuka 19 da suka danganci safarar kudaden haram, cin amana da facaka da dukiyar gwamnati Naira biliyan N80.2 a zamanin mulkinsa.
Hukumar ta kasa gurfanar da shi a ranar 18 ga wata saboda rashin kama shi.
A lokacin zaman ne kuma lauyansa, Abdulwahab Mohammed, ya shaida wa wa alkalin, Emeka Nwite, cewa ba shi da hurumin ba da umarnin kama wanda yake karewa.