EFCC ta kai samame Jami’ar Dan Fodio, ta yi awon gaba da ɗalibai

Ya zuwa yanzu dai ba a san takamaiman dalilin kai samamen ba.

EFCC ta kai samame Jami’ar Dan Fodio, ta yi awon gaba da ɗalibai

Jami’an Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arziƙi Zagon Ƙasa (EFCC), sun kai samame ɗakunan kwanan ɗalibai na Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Jihar Sakkwato (UDUS), inda suka kama wasu ɗalibai

Sun kai samamen ne da safiyar ranar Asabar a unguwannin Kwakwalawa da Gidan Yaro, unguwannin da galibin daliban jami’ar ne ke zama.

Wasu sun wa Aminiya cewar jami’an EFCC sun kai samamen da misalin ƙarfe karfe 4 na asuba, inda suka shiga ɗakunan ɗalibai suna kama su.

Wani ɗalibi ya ce, “Sun zo da asuba, suka shiga ɗakunanmu, suka fara kama mu ba tare da sun faɗa mana dalili ba.”

Sai dai har yanzu, EFCC ba ta fitar da wata sanarwa dangane da samamen ko kuma dalilin kama ɗaliban ba.

Wannan lamari yana kama da wani samame da jami’an hukumar suka kai a Jami’ar Fasaha ta Tarayya, Akure (FUTA) da ke Jihar Ondo a watan Fabrairu, inda suka ɓalle ɗakunan kwanan ɗalibai da tsakar dare.

Sun kama ɗalibai da misalin ƙarfe 2 na dare a wajen jami’ar.

Yayin wannan samamen, ɗaliba da dama sun ɗauka jami’an EFCC ɗin masu garkuwa da mutane ne saboda yadda suka yi amfani da ƙarfin tuwo wajen shiga dakunansu.

Rahotanni sun bayyana cewa jami’an da suka fito daga ofishin EFCC na yankin Benin, sun lalata kayayyaki tare da cin zarafin ɗaliban, ciki har da ‘yan mata.

Aminiya ta ruwaito cewar bayan kai samamen, Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya dakatar da jami’an hukumar daga kai irin waɗannan samame cikin dare.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos