EFCC ta kama Bobrisky kan wulaƙanta takardun kuɗi
An gayyaci Bobrisky bayan ɓullar wani bidiyo da ke nuna yadda yake yin liƙi da sabbin banduran takardun naira.
Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon ƙasa ta kama Idris Okuneye da aka fi sani da Bobrisky saboda zarginsa da wulaƙanta takardun kuɗi na naira.
Hakan na ƙunshe cikin wani saƙo da EFCC ta wallafa a shafinta na X a ranar Alhamis.
- Akwai rashin tausayi a ƙarin kuɗin wutar lantarki da gwamnati ta yi — NLC
- Biyan kuɗin shiga Itikafi a Masallatai bidi’a ce — Sheikh Maqari
EFCC ta bayyana cewa ta gayyaci Bobrisky bayan ɓullar wani bidiyo da ke nuna yadda mai shekara 31 a duniyar ke yin liƙi da sabbin banduran takardun naira.
Hukumar ta ce bidiyon ya naɗo Bobrisky yana watsi da takardun kuɗin a bikin nuna wani fim mai suna Ajakaju wanda jarumar Nollywood, Eniola Ajao ta shirya da aka yi ranar 24 ga watan Maris a shagon Film One Circle Mall da ke Lekki a Jihar Legas.
Sanarwar ta ce a baya ma an samu Bobrisky da aikata laifin da ake zargi a wasu tarukan sharholiya, kamar yadda EFCC ta ce bincike ya nuna.
A cewar hukumar, Bobrisky ya amsa gayyatar da ta yi masa kuma da safiyar ranar Laraba ya bayyana a ofishinta na Legas domin amsa tambayoyi.
EFCC ta ce ba da daɗewa ba za a gurfanar da Bobrisky a gaban kotu.