EFCC ta kama kwamandan Peace Corps na Gombe
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati ta Najeriya, EFCC ta kama Kwamandan kungiyar samar da zaman lafiya ta Najeriya wato ‘Nigerian Peace Corps’ Ambrose Enoch, na jihar Gombe. An dai kama kwamandan ne akan zargin karbar kudade daga wajen jama’a masu neman aikin kungiyar. Majiyarmu ta gano cewa, hukumar […]
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati ta Najeriya, EFCC ta kama Kwamandan kungiyar samar da zaman lafiya ta Najeriya wato ‘Nigerian Peace Corps’ Ambrose Enoch, na jihar Gombe.
An dai kama kwamandan ne akan zargin karbar kudade daga wajen jama’a masu neman aikin kungiyar.
Majiyarmu ta gano cewa, hukumar EFCC ta kama Kwamandan ne a reshen ofishin Peace Corps na Jihar Gombe akan tuhumar karbar kudade don samar wa masu sha’awa shiga gurbi, kudin dai sun hada da: kudin horarwa da kudin kakin qungiyar da ya kai naira miliyan 54.