EFCC ta kama masu cuwa-cuwar tikitin jirgin kasa a Abuja da Kaduna

A ranar Asabar da ta gabata ce Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC)  ta kama mutum biyar bisa zarginsu da yin cuwa-cuwa wajen sayar da tikitin jirgin kasa. Wadanda Hukumar EFCC ta kama sun hada da Clement Zakka da Udim Sunday Samson da Adams Danladi da Otitomoni Omobolanle da kuma Hassan Dauda. Haka […]

EFCC ta kama masu cuwa-cuwar tikitin jirgin kasa a Abuja da Kaduna

Waxansu daga cikin waxanda EFCC ta kama kan zargin cuwa-cuwar tikitin jirgin qasa a Abuja

A ranar Asabar da ta gabata ce Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC)  ta kama mutum biyar bisa zarginsu da yin cuwa-cuwa wajen sayar da tikitin jirgin kasa.

Wadanda Hukumar EFCC ta kama sun hada da Clement Zakka da Udim Sunday Samson da Adams Danladi da Otitomoni Omobolanle da kuma Hassan Dauda.

Haka a washegari Lahadi  Hukumar EFCC a Kaduna ta yi nasarar kama wadansu bisa zargin hada baki wajen yin cuwa-cuwar sayar da tikiti ga fasinjoji ba bisa ka’ida ba a tashar jirgin kasa na Rigasa.

Hukumra ta ce ta samu nasarar kama wadannan mutane ne bayan ta samu bayanan sirri da suka nuna suna yin cuwa-cuwa wajen sayar da tikitin ga fasinjoji a tasohin jirgin kasan da ke Idu da Kubwa a Babban Birnin Tarayya, Abuja da kuma tashar jirgin kasa da ke Rigasa, Kaduna wanda hakan ya sa da yawa daga cikin fasinjoji suke shan wuya kafin su samu tikitin shiga jirgin.  “Wannan ya saba wa kudirin Gwamnatin Tarayya na ganin ta samar da hanyoyin sufuri ga al’umma cikin sauki,” inji EFCC.

Bincike ya nuna cewa wadansu ma’aikatan tashar jirgin suna hada baki da ’yan gada-gada wajen tsawwala wa tikitin kudi.

Alal misali, tikitin da ake sayar da shi a kan Naira 1,300  zuwa Naira 1,500 an koma ana sayar da shi ne a tsakanin Naira 2000 zuwa Naira 5000.  Yayin da tikitin alfarma (First Class) da ake sayar da shi a kan Naira 2,500 an koma ana sayar da shi a bayan fage a kan Naira 7000 zuwa Naira dubu 15.

A tashar jirgin ta Rigasa Kaduna Hukumar EFCC ta ce ta samu nasarar kama wani ma’aikaci daya ne tare da ’yan gada-gada biyu.  Haka hukumar ta tuhumi Manajan tashar jirgin da jami’in da ke kula da bangaren kasuwanci da kuma jami’in da ke kula da sayar da tikitin don samun karin bayani.

Hukumar ta ce da zarar an kammala bincike za a tura ma’aikatan da masu cuwa-cuwar tikitin da aka kama zuwa kotu don a yanke musu hukunci.

Ɗalibai da malamai da aka sace a Oyo sun kuɓuta

Sojoji sun daƙile yunƙurin mayaƙan ISWAP a Borno

An ceto ma’aikacin INEC da aka yi garkuwa a Zamfara

Za a gurfanar da mutum biyu don shan taba a jirgin sama