EFCC ta tsare masu sayar da sabbin takardun kudi a Kano
EFCC ta kama ’yan kasuwa da jami’an banki kan sayar da sabbin takardun Naira a Jihar Kano
Hukumar EFCC mai yaki da masu karya tattalin arzikin kasa ta tsare wasu ma’aikatan banki su shida kan zargin sayar da sabbin takardun kudi na Naira a Jihar Kano.
Jami’an hukumar EFCC sun kuma kama wasu ’yan kasuwa biya da ke harkar sayar da sabbin sabbin takardun kudin a jihar Kano.
Kakakin EFCC Dele Oyewale, ya ce an kama mutanen su 11 ne a ranar Litinin, bayan samun bayanan sirri kan harkallar da suke gudanarwa.
Jami’in ya bayyana cewa a yayin da ’yan kasuwar ke sayar wa jama’a sabbin takardun kudi, ma’aikatan banki kuma an kama su ne kan sayar da takardun kudin ga ’yan kasuwar da aka kama.
Hukumar ta ce za a gurfanar da dukkan mutanen 11 a gaban kotu nan ba da jimawa ba, idan aka kammala bincike.