EFCC ta kama Murja Kunya kan wulaƙanta takardun Naira
Za a gurfanar da ita a kotu domin fuskantar hukunci bisa laifin da ake zarginta da aikatawa.

Rahotanni sun bayyana cewa Hukumar EFCC reshen Jihar Kano ta cafke shahararriyar jarumar nan ’yar TikTok, Murja Ibrahim Kunya.
Bayanai sun ce hukumar mai yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya ta’annati ta cafke Murja Kunya bisa zargin wulaƙanta takardar Naira.
- NAJERIYA A YAU: Guraben Ayyukan Da Aka Kasa Cikewa A Najeriya
- El-Rufai ya nemi afuwa ko mu maka shi a kotu — Gidauniyar Ɗahiru Bauchi
Wata majiya daga EFCC ta tabbatar da cewa an kama Murja a ranar Asabar a Kano, kuma ana ci gaba da bincike kan lamarin, a cewar Gidan Rediyon Freedom da ke Kano.
Majiyar hukumar ta ce idan bincike ya kammala, za a gurfanar da ita a kotu domin fuskantar hukunci bisa laifin da ake zarginta da aikatawa.
Rahotanni sun nuna cewa an kama Murja kimanin makonni uku da suka gabata, amma ta tsere daga beli kafin sake kama ta a ranar Asabar ɗin.
Murja Kunya ta yi kaurin suna tun bayan fara amfani da kafafen sada zumunta a matsayin abin barkwanci, kafin daga bisani ta mayar da shi dandalin sana’a.
A tsawon lokaci, ta shahara musamman a TikTok, inda take amfani da sunan “Yagayagamen,” duk da cewa a bayan nan ta jawo ce-ce-ku-ce a kanta.
A bayan nan dai hukumar ta EFCC ta cafke wasu abokan sana’ar Murja ’yan TikTok irinsu Alamin G-Fresh da Ashir Idris kan makamancin wannan zargi na wulaƙanta takardun kuɗi.