EFCC ta kama mutum 48 masu yin damfara ta yanar gizo a Kaduna

Hukumar yaki da Cin hanci da Rashawa ta EFCC ta ce, ta kama wasu da take zargin masu yi wa jama’a damfara ne ta yanar gizo su 48 a moboyarsu a da ke Kaduna. Shugaban Hukumar EFCC na jihar, Mailafia Yakubu ne ya sanar da hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa. […]

EFCC ta kama mutum 48 masu yin damfara ta yanar gizo a Kaduna

Jami’an EFCC a bakin aiki

Hukumar yaki da Cin hanci da Rashawa ta EFCC ta ce, ta kama wasu da take zargin masu yi wa jama’a damfara ne ta yanar gizo su 48 a moboyarsu a da ke Kaduna.

Shugaban Hukumar EFCC na jihar, Mailafia Yakubu ne ya sanar da hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa.

Ya kuma kara da cewa, daya daga cikin wadanda aka kama sunansa na cikin hukumar tsaron kasar Amurka watau FBI  da ake nama saboda zarginsa da laifin aikata cuta ta yanar gizo.

Mailafia, ya ce hadin gwiwa tsakanin Hukumar EFCC da FBI ta kasar Amurka ya taimaka masu wajen kwato dalar Amurka dubu 373‎ da kuma sama da Naira miliyan 373 a kokarinsu na yaki da cuta a yanar gizo.

Ya ce, sun gano Naira miliyan 373 ne a wasu bankuna masu zaman kansu kuma an bibiye masu su an kuma kwato kudaden.

Ya kuma kara da cewa, Hukumar rashen jihar Kaduna ta samu nasarar kwato dalar Amurka dubu 48 da kuma sama da Naira miliyan 198 duk a bin cikenta.

Ya ce, a yanzu haka kotu ta hukunta 23 daga cikinsu, yayin da kuma sauran ana ci gaba da bin cikensu.

“Sannan kuma daga watan Janairu zuwa yau, hukumar rashen jihar ta Kaduna ta samu takardun koke dari 345, sannan 286 an amince da’a yi bincike, 52 kuma an mikasu sashen shari’a da hukunci na hukumar sai 56 kuma suna gaban kotu.‎

Dan haka sai ya shawarci masu ruwa da tsaki musamman yan jaridu da su hada hannun da hukumar wajen yaki da Cin hanci da Rashawa a kasar nan.