EFCC ta kama tagwaye ’yan yahoo
Wasu tagwaye sun fada komar EFCC bisa zargin su da laifin damfarar mutane ta intanet wanda aka fi sani da yahoo boys
Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arziki tu’annati (EFCC), ta kama wasu tagwaye maza kan zargin damfara ta intanet, yahoo boys.
EFCC shiyyar Ibadan ta kama su ne a kauyen Apete kusa da Ibadan babban birnin Jihar Oyo, tare da wasu matasa biyar da ake zargin ’yan Yahoo-yahoo ne.
Hukumar ta ce rundunar ’yan sandan jihar ta mika mata wasu matasa uku da ’yan sandan suka kama bisa irin wannan zargi a lokacin da suke yin sintiri a Ibadan.
An sallami daya daga cikinsu ba tare da beli ba, bayan an gano ba ya cikin tawagar tasu.
- Yadda ’yan bindiga suka sace mutane 30 a Abuja
- Yadda aka karrama mai Keke-NAPEP Da Ya Dawo Da N9m da ya tsinta a babur dinsa a Yobe
Kuma an gano wata karamar mota kirar Toyota Corolla da iPhone guda 11 da sauran wayoyin salula.
Hukumar ta ce da zarar ta kammala bincike za a gurfanar da wadanda ake zargin gaban kotu domin yanke masu hukunci.