EFCC ta kama tsohon Gwamnan Taraba kan zambar N27bn

EFCC ta kammala tattara aƙalla tuhume-tuhume 15 na zamba a kan tsohon gwamnan.

EFCC ta kama tsohon Gwamnan Taraba kan zambar N27bn

Gwamnan Taraba, Darius Dickson Ishaku

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta cafke tsohon Gwamnan Jihar Taraba, Darius Ishaku kan zargin aikata zambar Naira biliyan 27.

Rahotanni sun bayyana cewa, a wannan Juma’ar ce jami’an EFCC suka yi dirar mikiya a gidan tsohon gwamnan da ke Abuja wanda wa’adinsa ya ƙare a shekarar 2023 bayan shafe tsawon shekaru takwas a kan madafun iko.

Aminiya ta ruwaito daga wata majiya a hukumar ta EFCC na cewa har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, gwamnan yana hannun hukumar inda ake titsiye shi.

Majiyar ta bayyana cewa hukumar ta EFCC ta kammala tattara aƙalla tuhume-tuhume 15 da ake zargin tsohon gwamnan kuma nan ba da jimawa ba zai gurfana a gaban kuliya.

Rikicin Masarautar Kano: Tsagin Aminu Ado Bayero zai ɗaukaka ƙara

Yadda Jimmy Carter ya ceto rayuwata – Obasanjo

Sojoji sun lalata sansanin Bello Turji, sun kuɓutar da mutum 7

Wani mutum ya rasu yayin gyaran rijiya a Kano