EFCC ta kama tsohon Gwamnan Jihar Kaduna

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Hana Yi wa Tattalin Arziki Ta’annati (EFCC) ta cafke tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Muktar Ramalan Yero da kuma tsohon mai neman takarar gwamnan Jihar Kano a  karkashin jam’iyyar PDP, Alhaji Salihu Sagir Takai, jiya Litinin. An ce an kama ‘yan siyasar biyu ne saboda ana zargin sun da karba […]

EFCC ta kama tsohon Gwamnan Jihar Kaduna
EFCC ta kama tsohon Gwamnan Jihar Kaduna

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Hana Yi wa Tattalin Arziki Ta’annati (EFCC) ta cafke tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Muktar Ramalan Yero da kuma tsohon mai neman takarar gwamnan Jihar Kano a  karkashin jam’iyyar PDP, Alhaji Salihu Sagir Takai, jiya Litinin.

An ce an kama ‘yan siyasar biyu ne saboda ana zargin sun da karba kudin kamfe daga tsohuwar Ministar Albarkatun Man Fetur Deizani Alison Madueke har Naira biliyan 23 . Har ila yau, ana tsare da Sakataren jam’iyyar PDP a Jihar Kano,  Alhaji Auwalu Ibrahim Danzabuwa, an ruwaito cewa mutanen biyu suna tsare ne a ofishin shiyya na Hukumar EFCC da ke Jihar Kano.