EFCC ta kama tsohon Ministan Buhari na Lantarki

Ana zargin tsohon Ministan da almundahanar naira biliyan 22.

EFCC ta kama tsohon Ministan Buhari na Lantarki

Hukumar Yaki da Yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati a Najeriya (EFCC) ta kama tsohon Ministan Lantarki, Injiniya Saleh Mamman.

Rahotanni na cewa EFCC ta kama Saleh Mamman ne tun da sanyin safiyar Laraba inda ake ci gaba da tsare da shi a shalkwatar hukumar da ke Abuja.

Sun ce kamen na da alaka da zargin almundahanar wasu kudade kimanin naira biliyan 22.

Zuwa yanzu, ba a ji wani martani daga ministan ko wasu makusantansa ba.

Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa jami’an EFCC sun kama Saleh Mamman ne game da jerin bincike a kan zargin aiwatar da wasu ayyukan lantarki.

Rahotanni sun ce ana zargin tsohon ministan da hada baki da wasu jami’ai a Ma’aikatar Lantarki wadanda ke kula da asusun ajiyar kudaden ayyuka a tashoshin lantarki na Mambilla da Zungeru, don karkatar da naira biliyan 22, tare da rabawa a tsakanin su.

Bayanai sun ce bincike ya bankado wasu kadarori a Najeriya da kasashe waje masu alaka da jami’an da ake zargi, sannan an ba da rahoton gano miliyoyin nairori da daloli.

A ranar 1 ga watan Satumban 2021 ne Shugaba  Buhari ya sallami ministan na lantarki bayan nada shi a watan Agustan 2019.

Matakin sallamar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban, Femi Adesina ya fitar bayan taron majalisar koli.

Matakin wani bangare ne na sauye-sauyen da shugaba Buhari ke aiwatarwa, a cewar Femi Adesina.