EFCC ta kama tsohon Ministan Lantarki Saleh Mamman

A makon jiya ne Kotu ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekara 75 bayan samunsa da laifin satar kuɗi sama da naira biliyan 33.

EFCC ta kama tsohon Ministan Lantarki Saleh Mamman

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa EFCC ta kama tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, bayan shafe kwanaki ana neman shi.

Bayanai sun ce an kama shi ne a unguwar Rigasa da ke Jihar Kaduna tare da wasu mutane biyu da ake zargin suna ba shi kariya.

Da yake yi wa manema labarai ƙarin haske, Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya ce an cafke tsohon ministan ne da misalin ƙarfe 3:30 na dare.

A ranar Laraba, 13 ga watan Mayu, 2026 ne dai Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa Saleh Mamman hukuncin ɗaurin shekara 75 a gidan yari, bayan samunsa da laifin satar kuɗi sama da naira biliyan 33.