EFCC ta kama wanda FBI ke nema da wasu mutum 47 bisa zargin zamba ta yanar gizo a Kaduna

  Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta ce ta kama wadansu da take zargin masu zamba ne ta Intanet su 48 a maboyarsu da ke Kaduna. Shugaban Hukumar a Jihar Kaduna, Malam Mailafia Yakubu ne ya sanar da haka lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa. Ya ce daya […]

EFCC ta kama wanda FBI ke nema da wasu mutum 47 bisa zargin zamba ta yanar gizo a Kaduna

Muqaddashin Shugaban Hukumar EFCC Ibrahim Magu

 

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta ce ta kama wadansu da take zargin masu zamba ne ta Intanet su 48 a maboyarsu da ke Kaduna.

Shugaban Hukumar a Jihar Kaduna, Malam Mailafia Yakubu ne ya sanar da haka lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa.

Ya ce daya daga cikin wadanda aka kama sunansa na cikin wadanda Hukumar FBI ta Amurka ke nema.

Malam Mailafia ya ce hadin gwiwa a tsakanin EFCC da Hukumar FBI ta kasar Amurka ya taimaka musu wajen kwato Dalar Amurka dubu 373 da sama da Naira miliyan 373 a kokarinsu na yaki da zamba ta Intanet.

Ya ce a yanzu haka kotu ta hukunta 23 daga cikinsu, yayin da kuma sauran ana ci gaba da bincike a kansu.

“Daga watan Janairu zuwa yau, Hukumar EFCC a Jihar Kaduna ta samu takardun koke 345, sannan 286 an amince a yi bincike a kai, 52 kuma an mika su ga sashen shari’a da hukunci na hukumar sai 56 da suke gaban kotu,” inji shi.

Don haka sai ya shawarci masu ruwa da tsaki musamman ’yan jarida su hada hannun da hukumar wajen yaki da cin hanci da rashawa.