EFCC ta kama Yahaya Bello

Wasu rahotanni sun ce tsohon gwamnan da kansa ya je ofishin hukumar.

EFCC ta kama Yahaya Bello

Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arziƙi Zagon Ƙasa (EFCC), ta kama Tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, kan zargin karkatar da kuɗaɗe.

Rahotanni sun bayyana cewar jami’an EFCC na yi masa tambayoyi a halin yanzu.

Sai dai a gefe guda, an samun rahotanni masu karo da juna kan yadda ya isa ofishin EFCC – wasu na cewa an kama shi, yayin da wasu ke nuna cewa tare da lauyoyinsa ya isa ofishin hukumar.

A zaman kotu na baya na ranar 14 ga watan Nuwamba, EFCC ta nemi a ɗage ƙarar zuwa ranar 27 ga watan Nuwamba.

EFCC, ta ce wa’adin kwana 30 na sammaci da aka bayar na nan bai ƙare ba.

Idan ba a manta ba Yahaya Bello, ya shiga wasan ɓuya tsakaninsa da EFCC tun bayan da ya sauka daga mulki.

Duk da zarge-zargen da EFCC ke masa na karkatar da kuɗaɗe a lokacin da yake mulkin Jihar Kogi, Bello ya musanta aikata hakan.

An bankaɗo inda ake sauya wa shinkafar tallafi buhu a Kano

Tinubu ya yaba wa NNPCL kan farfaɗo da matatar mai ta Fatakwal

EFCC ta kama Yahaya Bello

Yau za a fara lodin fetur daga Matatar Fatakwal —NNPC