EFCC ta kama ’yan yahoo 89 a gidan rawa

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) shiyyar Ibadan ta kama mutum 89 a karshen makon jiya lokacin da jami’anta suka kai samamen ba-zata a wani gidan rawa da aka fi sani da Club 360 da ke kan babbar hanyar Akala a Unguwar Oluyole a birnin Ibadan. Bayanin haka yana kunshe ne cikin […]

EFCC ta kama ’yan yahoo 89 a gidan rawa

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) shiyyar Ibadan ta kama mutum 89 a karshen makon jiya lokacin da jami’anta suka kai samamen ba-zata a wani gidan rawa da aka fi sani da Club 360 da ke kan babbar hanyar Akala a Unguwar Oluyole a birnin Ibadan.

Bayanin haka yana kunshe ne cikin wata sanarwa da Kakakin Hukumar Mista Tony Orilade ya sanya wa hannu da aka raba wa ’yan jarida a ranar Litinin da ta gabata a Ibadan, inda ya ce sun samu labarin sirri ne a kan wannan gidan rawa da ake zargin maboyar masu sata ta Intanet ne da aka fi sani da ’yan yahoo ne da suke cin karensu babu babbaka a fannin damfarar jama’a miliyoyin kudi.

Hakan ne ya sa jami’an hukumar suka shiri domin yi wa gidan dirar mikiya inda suka yi nasarar kama wadannan mutane.

Kayayyakin da aka samu tare da wadanda ake zargin sun hada da kananan motoci iri-iri da na’urorin kwanfuta da wayoyin salula masu tsada da makamantansu.