EFCC ta saki Tambuwal
Tsare Tambuwal da EFCCn ta yi ya janyo ce-ce-ku-ce a ƙasar, musamman tsakanin ’yan hamayya.
Aminu Waziri Tambuwal
Tsohon Gwamnan Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ya shaƙi iskar ’yanci bayan sakinsa da Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya ta’annati ta yi a yammacin wannan Talatar.
A jiya Litinin ce aka ruwaito cewa EFCC ta tsare Tambuwal a hedikwatarta da ke Abuja, inda take zargin ya fitar da wasu kuɗaɗe ba bisa ƙa’ida ba har naira biliyan 189 a lokacin da yake riƙe da madafan iko.
- Bankin Duniya zai kashe $300m domin inganta rayuwar ’yan gudun hijira a Arewacin Nijeriya
- Dasuki: Kotu ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kammala shari’ar kuɗin makamai
Hakan na zuwa ne bayan tsohon gwamnan ya amsa goron gayyatar EFCC da misalin ƙarfe 11:16 na safiyar ranar Litinin, amma daga bisani hukumar ta tsare shi bayan ya gaza amsa wasu tambayoti dangane da zargin fitar da kuɗaɗen da take yi masa.
Da yake tabbatar da lamarin, wani jami’in EFCCn ya ce sun bayar da belin tsohon gwamnan wanda da zarar ya cika sharuɗan da aka gindaya zai shaƙi iskar ’yanci.
Tsare Tambuwal da EFCCn ta yi ya janyo ce-ce-ku-ce a ƙasar, musamman tsakanin ’yan hamayya, waɗanda ke zargin hakan na da alaƙa da rawar da yake takawa a tafiyar ’yan jam’iyyar haɗaka ta ADC.
Cikin saƙon da Tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya Atiku Abubakar ya wallafa wannan Talatar a shafinsa na X, ya ya zargi gwamnatin Bola Tinubu da amfani da Hukumar EFCC wajen yi wa masu adawa da ita barazana.
A cewar Wazirin Adamawa, “dalilin da EFCC ta tsare tsohon Gwamnan Sakkwato, Sanata Aminu Waziri Tambuwal, shi ne saboda yana cikin jam’iyyar adawa ta haɗaka.
“Wannan yana ƙara nuna yadda gwamnatin Tinubu ke ci gaba da yaɗa manufofinta na musgunawa, tsoratarwa, da rusa ‘yan adawa.”
Ya ƙara da cewa, “A yau dai duk wanda yake da alaƙa da ‘yan adawa to za a zarge shi da cin hanci da rashawa.
“Kuma da zarar an tilasta musu komawa kan tsarin tafiyar siyasar Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu, sai ya zama kamar an gafarta musu zunubansu ne.”