EFCC ta samu Naira biliyan biyu da rabi a asusun ’yar aikin Stellah Oduah
Jami’an Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin kasa Tu’annati (EFCC) sun gano kimanin Naira biliyan biyu da rabi a wani asusun ajiyar banki da aka bude da sunan wata ’yar aikin gida ga tsohuwar Ministar Sufurin Jiragen Sama, Misis Stella Oduah, wadda yanzu Sanata ce daga Jihar Anambra.Kafar labarai ta Sahara Reporters ta fadi […]
Jami’an Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin kasa Tu’annati (EFCC) sun gano kimanin Naira biliyan biyu da rabi a wani asusun ajiyar banki da aka bude da sunan wata ’yar aikin gida ga tsohuwar Ministar Sufurin Jiragen Sama, Misis Stella Oduah, wadda yanzu Sanata ce daga Jihar Anambra.
Kafar labarai ta Sahara Reporters ta fadi a ranar Lahadin da ta gabata cewa wasu manyan majiyoyi biyu na Hukumar EFCC sun shaida wa wakilinta cewa an bude asusun ajiyar tare da jibge wannan dimbin kudi ne ba tare da sanin ’yar aikin tsohuwar ministar ba. “Ga alama Sanata Oduah ta bude asusun ne da suna da hoto da bayanan ’yar aikinta ba tare da ’yar aikin ta san komai a kai ba,” inji wani ma’aikacin Hukumar EFCC da yake da masaniya kan badakalar.
Wata majiyar Hukumar EFCC ta shaida wa kafar cewa Misis Oduah tana ta bin kan wadansu jami’an gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari tana kamun kafa domin a kashe maganar don hana gurfanar da ita a gaban kotu. Majiyar ta ce a makon jiya ta nemi ta gana da Shugaban Hukumar EFCC Ibrahim Magu, tana da’awar cewa tana son ganawa da shi ne a hukumance a matsayinta na Sanata.
Majiyoyin biyu na Hukumar EFCC da suka bayyana wa kafar kan asusun ’yar aikin da aka gano sun ce, Misis Oduah ce kadai take sanya hannu wajen tafiyar da asusun, inda suka ce suna kokarin gano yadda tsohuwar ministar ta yi badakalar wannan dimbin kudi.
“Zuwa makon jiya asusun yana ci gaba da aiki dauke da Naira biliyan biyu da rabi,” inji daya daga cikin majiyoyin na EFCC. Sai dai majiyar ta ce ba za ta iya hakkakewa ko Shugaban Hukumar wanda yake Umara a Saudiyya ya bayar da umarni a rufe asusun ba.
daya majiyar ta EFCC ta bayyana cewa gano asusun “’yar aikin” na nufin mai yiwuwa tsohuwar ministar ta saci kudin da ya kai Naira biliyan biyar da miliyan 600 ke nan daga asusun Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama a lokacin da take minista.
Rahoto na farko da SaharaReporters ta bayar ya ce masu bincike na Hukumar EFCC sun gano cewa Misis Oduah ta rarraba Naira biliyan 3 da miliyan 600 da ta mallaka ta haramtacciyar hanya ta yin amfani da kamfanoni takwas.
Sai dai a martanin da tsohuwar Ministar ta mayar ta ofishinta da jaridar Premium Times ta ruwaito a ranar Litinin, ta ce rahoton “gaba dayansa karya ne bai da tushe.”
Wata sanarwa dauke da sanya hannun shugabar sashin sadarwarta mai suna Francisca Onyeisi, ta ce Misis Oduah ta ce in da labarin gaskiya ne, da tuni an kama ta, musamman a lokacin da EFCC “take rufe asusunan bankuna tare da takura wa gwamnonin ’yan adawa da su ma suke da kariya kamar ta Shugaban kasa.”
Tsohuwar Minsitar ta nemi magoya bayanta da sauran jama’a su yi watsi da rahoton, inda ta ce ta “samu kudi ne a harkar mai da gas da aikin gona kafin ta shiga siyasa.”
A watan Fabrairun shekarar 2014 ne aka salami Misis Oduah daga mukaminta bayan an same ta da laifin karbar motoci masu sulke kirar BMW da suka kai na Naira miliyan 255 a lokacin daga wata hukuma da take karkashin kularta.
A watan Agustan bara, Misis Oduah ta garzaya wata Kotun Tarayya tana neman a hana EFCC bincikarta kan batun motocin masu sulke inda alkalin kotun Mai shari’a Mohammed Yunusa, ya biya mata bukatar, sai dai bayan an yi masa sauyin wurin aiki, sai wani alkalin Kotun Tarayyar ya soke umarnin, inda ya ba EFCC izinin gudanar da binciken.