EFCC ta sanya Kwankwaso zaman kulle – Lauyansa

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta tilasta wa tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso zaman kulle a gidansa tare da hana shi yin walwala, sakamakon barazanar kama shi da take yi a baya-bayan nan. Lauyan tsohon Gwamnan Ekechikwu Eze ne ya yi wannan korafi a gaban Babbar Kotun Jihar […]

EFCC ta sanya Kwankwaso zaman kulle – Lauyansa
EFCC ta sanya Kwankwaso zaman kulle – Lauyansa

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta tilasta wa tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso zaman kulle a gidansa tare da hana shi yin walwala, sakamakon barazanar kama shi da take yi a baya-bayan nan.

Lauyan tsohon Gwamnan Ekechikwu Eze ne ya yi wannan korafi a gaban Babbar Kotun Jihar Kano da ke garin Gezawa, inda ya nemi kotun ta ja wa hukumar layi kan kokarin da take yin a kama wanda yake karewa.
A cewar Lauya Eze, jami’an Hukumar ta EFCC na bin Sanata Kwankwaso sau da kafa da niyyar kama shi, inda hakan ya sa tsohon Gwamnan ya kasa sukuni, ko fita zuwa ofishinsa da ke Majalisar Tarayya ba ya iya yi, sai dai zaman gida.
Bayan saukar Sanata Kwankwaso daga Gwamna ya kai ziyara ofishin EFCC don amsa tambayoyi kan wasu kudi da kungiyar ’yan fansho ta Jihar Kano ke zargin ya karkatar daga asusun fansho don wasu ayyuka a lokacin da yake Gwamna.
Bayan sauraron korafin na Sanata Kwankwaso Babbar Kotun ta Jihar Kano ta dakatar da Hukumar EFCC daga kama Sanata Kwankwaso wanda aka ce ya rufe kansa a gida tsawon kwana biyu, inda ta dage sauraron shari’ar zuwa 15 ga watan Yuli.
Alkalin Kotun Mai shari’a Muhammad Yahya ne ya haramta wa EFCC kama Kwankwaso har sai kotun ta kammala bincikenta inda a zama na gaba kotu za ta gayyaci Hukumar EFCC domin sauraren karar.
Kotun ta ce ba za ta yi aiki da jita-jita ba, har sai abin da sakamakon binciken ta ya tabbatar.