EFCC zata ci gaba da gurfanar da Diezani a gaban kotu

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati EFCC ta ce za ta gurfanar da tsohuwar ministar man fetur ta  Najeriya, Misis Diezani Alison-Madueke a gaban babbar kotun tarayya da ke unguwar Apo Abuja kan zargin cin hanci da rashawa. A ranar 25 watan Fabrairun 2019 ne za a gurfanar da […]

EFCC zata ci gaba da gurfanar da Diezani a gaban kotu

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati EFCC ta ce za ta gurfanar da tsohuwar ministar man fetur ta  Najeriya, Misis Diezani Alison-Madueke a gaban babbar kotun tarayya da ke unguwar Apo Abuja kan zargin cin hanci da rashawa.

A ranar 25 watan Fabrairun 2019 ne za a gurfanar da Misis Alison-Madueke da kuma tsohon shugaban kamfanin tatar mai na Atlantic Energy Drilling Company, Jide Omokore kan zargin aikata laifuka biyar. Kamar yadda mai magana da yawun hukumar EFCC Mista Tony Orilade ya sanar wa manema labarai.