EFCC za ta gabatar da ayyukan da ta yi karkashin Magu

Kwamitin da Shugaban Kasa ya nada karkashin Mai Shari’a Ayo Salami, kan binciken Ibrahim Magu, ya umurci daraktoci da wasu manyan jami’an Hukumar Yaki da masu yi wa Tattalin Arzikin Ta’annati (EFCC) su gabatar da ayyukan da suka gudanar cikin shekara biyar. Daga cikin wadanda suka gurfana gaban kwamitin, akwai Sakataren hukumar Olanipekun Olukoyede. Wakilin […]

EFCC za ta gabatar da ayyukan da ta yi karkashin Magu

Kwamitin da Shugaban Kasa ya nada karkashin Mai Shari’a Ayo Salami, kan binciken Ibrahim Magu, ya umurci daraktoci da wasu manyan jami’an Hukumar Yaki da masu yi wa Tattalin Arzikin Ta’annati (EFCC) su gabatar da ayyukan da suka gudanar cikin shekara biyar.

Daga cikin wadanda suka gurfana gaban kwamitin, akwai Sakataren hukumar Olanipekun Olukoyede.

Wakilin Aminiya ya samu labarin cewar an gayyace su bayar da ba’asi kan tuhumar da ake yi wa Magu, an kuma kwashe akalla awanni sha biyu ana yi musu tambayoyi.

Wata majiya ta bayyana wa Aminiya cewar dakataccen mukaddashin shugaban hukumar, Ibrahim Magu, na gaban kwamitin amma aka fitar da shi domin daraktan ayyukan hukumar Mohammed Umar ya bayar da shaida.

Majiyar ta ce an umarci daraktocin su rattaba hannu ga kowane shafin rahoton ayyukansu kafin su gabatar wa kwamitin, sa’annan wadanda ke sashen kwato dukiyoyi a hannun barayin gwamnati su gabatar da rasidai da lambobin yawan dokiyoyin da aka kwato.

“Duba da yadda kwamitin ke gudanar da aikinsa, akwai yiwuyar za su ba shugaba Buhari shawarar yadda za a canja tsarin gudanarwar hukumar domin an umarci manyan jami’an wurin da su yi bayanin yawan ma’aikatan hukumar da kuma sunayen ‘yan lelen dakataccen Shuagaban Hukumar, watau ‘Magu boys'”, inji ta

Wata majiya ta tabbatar da cewa tsohon kwamishinan ‘yan sanda na Ondo da ya taba aiki da EFCC ya bayar da shaida.

Haka nan kuma wani tsohon Mataimakin Sufeto Janar na yan sanda da yake da masaniya kan abubuwan da ke gudana a EFCC ya yi wa daraktocin tsauraran tambayoyi.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Tags