EFCC za ta gayyaci Kwankwaso da Wamakko kan zargin almundahana

Kwanannan tsofaffin gwamnoni biyu da suke majalisar dattawa karkashin jam’iyyar APC za su bakunci hukumar yaki da ta’annutin kudi ta EFCC.   Aminiya ta ruwaito cewa hukumar ta EFCC za ta kama Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso na jam’iyyar APC daga jihar Kano da Aliyu Magatakardar Wamakko dan jam’iyyar APC daga jihar Sokoto kan zargin satar […]

EFCC za ta gayyaci Kwankwaso da Wamakko kan zargin almundahana

Kwanannan tsofaffin gwamnoni biyu da suke majalisar dattawa karkashin jam’iyyar APC za su bakunci hukumar yaki da ta’annutin kudi ta EFCC.
 
Aminiya ta ruwaito cewa hukumar ta EFCC za ta kama Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso na jam’iyyar APC daga jihar Kano da Aliyu Magatakardar Wamakko dan jam’iyyar APC daga jihar Sokoto kan zargin satar kudin gwamnati da farnatar da kudin jihohinsu yayin da suke mulki.
EFCC za ta gayyaci Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar Kano kan korafin da aka yi masa na karkatar  da fiye da Naira biliyan uku  na kananan hukumomin jihar, shi kuwa Wamakko, tsohon gwamnan jihar Sokoto ana sa ran ya yi bayani kan zargin da ake yi masa na satar kudin jihar da suka kai Naira bilioyan 15.
 
Wata majiya daga hukumar EFCC  ta tsaiguntawa Aminiya jiya cewa hukumar tana bincike kan korafe-korafen da aka mika mata kan gwamnonin biyu.