EFCC za ta gurfanar da Babachir a gaban kotu
Gwamnatin Tarayya ta tattara bayanan badakalar da tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Mista Babachir Lawal da wadansu mutum biyar suka yi. A watan Oktoban shekarar 2017 ne Shugaba Muhammadu Buhari ya kori Babachir Lawal daga mukaminsa bayan binciken rahoton da aka yi wanda Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta kan tuhumar da ake yi […]
Gwamnatin Tarayya ta tattara bayanan badakalar da tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Mista Babachir Lawal da wadansu mutum biyar suka yi.
A watan Oktoban shekarar 2017 ne Shugaba Muhammadu Buhari ya kori Babachir Lawal daga mukaminsa bayan binciken rahoton da aka yi wanda Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta kan tuhumar da ake yi masa na karkatar da wasu kudaden gwamnati wajen bayar da kwangila.
Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati, (EFCC) ta tattara laifuffuka 10 da take tuhumar tsohon sakataren wanda Offem Uket ya hada rahoton a ranar 30 ga Janairu, wanda ke nuna zahirin tuhumar da ake yi wa Babachir tare da Daraktan kamfanin Rholabision Engineering Ltd, Hamidu Dabid Lawal da Suleiman Abubakar da wadansu ma`aikatan kamfanin a kan damfarar kudade da kadarori, wanda aikata wannan laifin ya ketadokar rashawa ta sashi na 26 (1) (c) da sauran laifuffuka masu alaka da su, ta shekarar 2000 wadda ta tanadi hukunci a sashi na 12 na dokar.
Sauran wadanda ake tuhuma a Babbar Kotun Tarayya a Abuja akwai Apeh John Monday da kamfaninsa Josmoh Technologies Ltd, da kamfanin Rholabision Engineering Ltd, wanda Babachir yake rike da mukamin Darakta. Ana sa ran EFCC za ta gurfanar da su a gaban kotun a makon gobe.
Daya daga cikin laifuffukan da ake tuhumar Hamidu, Abubakar da kamfanin Rholabision wanda aka ba kwangilar cire ciyawa ta Naira miliyan 6.4 daga ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ta hanyar Kwamitin Shugaban Kasa kan Farfado da Arewa maso Gabas (PINE)
Hukumar EFCC na tuhumar Hamidu a kan laifuffuka 9, wanda Injiniya Babachir Lawal bai ba da kwangilar kai-tsaye ba, kamar yadda ya bai wa kamfanin Josmon Technologies Ltd. kwangilar a kan cire ciyawar da ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ta bayar, a karkashin kwamitin (PINE) a kan Naira miliyan 272.5.
Ana tuhumar Babachir Lawal da laifin karkatar da kudade wajen bai wa kamfanin Josmon Technologies Ltd kwangila.