EFCC za ta gurfanar da Babachir a gaban kotu yau
Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati, (EFCC) ta tsare tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Mista Babachir Lawal kuma a yau ne ake saran gurfanar da shi a gaban kotu akan tuhumar da ake yi masa. Hukumar EFCC dai za ta gurfanar da Babachir a babbar kotun tarayya da ke unguwar Maitama Abuja, wanda […]
Babachir Lawal
Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati, (EFCC) ta tsare tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Mista Babachir Lawal kuma a yau ne ake saran gurfanar da shi a gaban kotu akan tuhumar da ake yi masa.
Hukumar EFCC dai za ta gurfanar da Babachir a babbar kotun tarayya da ke unguwar Maitama Abuja, wanda ake saran mai shari’a Jude Okeke zai jagoranta.