EFCC za ta kwace kadarorin Patience Jonathan

Hukumar EFCC ta bukaci babban kotun Abuja ta kwace wasu kadarori mallakan Uwargidan tsohon shugaban kasa, Patience Jonathan. Lauyan hukumar, Mista Benjamin Manji ne ya mika bukatar a gaban kotu, inda y ace kotu ta mallaka wa hukumar ta EFCC kadarorin Gidauniyar Ariwabai Aruera Reachout mallakan Patience. Lauyan ya ce kotu ta mallaka wa Hukumar […]

EFCC za ta kwace kadarorin Patience Jonathan

Hukumar EFCC ta bukaci babban kotun Abuja ta kwace wasu kadarori mallakan Uwargidan tsohon shugaban kasa, Patience Jonathan.

Lauyan hukumar, Mista Benjamin Manji ne ya mika bukatar a gaban kotu, inda y ace kotu ta mallaka wa hukumar ta EFCC kadarorin Gidauniyar Ariwabai Aruera Reachout mallakan Patience.

Lauyan ya ce kotu ta mallaka wa Hukumar EFCC, Fuloti mai lamba 1960 Cadastral, yanki na A05, Maitama, da kuma Fuloti mai lamba 1350, yankin Cadastral, Abuja.

Hakanan kuma, Hukumar ta bukaci kotu ta hana masu kula da kadarorin sayarwa ko bayar da hayan kadarori.

Lauyoyin Patience Jonathan, Ifedao Adedipe (SAN) da Mike Ozekhome (SAN), sun bukaci kotu da ta dakatar da batun kwace kadarorin.

“Wannan Gidauniyar an mata ragista sama da shekara 10 da suke wuce a matsayin gidauniyar taimakon marayu, kuma ta dade tana gabatar da ayyukan taimako kamar yadda ta kuduri aniya, kamar su koyar da mata sana’o’i, biyan kudin asibiti musamman masu fama da ciwo koda, da kuma taimakon marasa galihu.

Bayan ya kammala sauraro karar, mai shara’a Nnamdi Dimgba, ya daga shara’ar zuwa ranar 11 da watan Nuwamba.