Eh, za ta iya
Wata rana wadansu mutane suna zaune a majalisa, cikinsu akwai wani attajiri, wanda ko ya yi karya babu mai karyata shi. Sai ya dubi mutanen nan na zaune ya ce masu: “Lokacin da muna zuwa farauta a daji, mun taba kwana 40 gaban wata bishiya saboda tsananin girmanta, gefenta akwai kura da ’ya’yanta, daga gefen […]
Wata rana wadansu mutane suna zaune a majalisa, cikinsu akwai wani attajiri, wanda ko ya yi karya babu mai karyata shi. Sai ya dubi mutanen nan na zaune ya ce masu: “Lokacin da muna zuwa farauta a daji, mun taba kwana 40 gaban wata bishiya saboda tsananin girmanta, gefenta akwai kura da ’ya’yanta, daga gefen guda akwai gada ita ma da ’ya’yenta amma ba su taba haduwa waje daya ba saboda girman bishiyar.” Ko da ya gama ba da labarin sai wani ya yi karaf ya ce: “Af, yau wannan abin mamaki ne? Mu a nan Katsina akwai wata tsuntsuwa wadda ta leko da kanta daga dandagoro zuwa Barikin Soja amma ba a gama ganin bindinta a dandagoro ba saboda girmanta.” Ko da shi ma ya gama sai attajirin nan ya yi karaf ya ce: “Kai raba mu da karya, idan akwai tsuntsuwa irin wannan ina za ta je ta kwana?” Sai shi kuma ya ce masa: “Ai saman waccan bishiyar da ka fada, can take zuwa ta kwana.” Sai shi kuma ya ce: “Eh, za ta iya yiwuwa kuma.”