Ekuatorial Guinea ta yi wa matan Najeriya kafar ungulu
Yanzu dai ta tabbata kungiyar kwallon kafa ta mata ta Najeriya Super Falcons ba za ta halarci gasar wasannin Olamfik da zai gudana a Brazil a shekara mai zuwa ba, bayan Ekuatorial Guinea ta fitar da Najeriya a gasar neman hayewa zuwa wasannin na Olamfik a ranar Lahadin da ta wuce.Kocin Falcons Christopher danjuma ya […]
Yanzu dai ta tabbata kungiyar kwallon kafa ta mata ta Najeriya Super Falcons ba za ta halarci gasar wasannin Olamfik da zai gudana a Brazil a shekara mai zuwa ba, bayan Ekuatorial Guinea ta fitar da Najeriya a gasar neman hayewa zuwa wasannin na Olamfik a ranar Lahadin da ta wuce.
Kocin Falcons Christopher danjuma ya kadu matuka a lokacin da ya kalli yadda Ekuatorial Guinea ta lallasa Najeriya da ci 3-1 a wasa zagaye na biyu a can kasar duk da Najeriya ce ta fara zura kwallon farko a farkon rabin lokaci na wasan. Wannan shi ne karo na biyu a jere da Najeriya ba ta halartar gasar ta Olamfik. A shekarar 2012 ma Kamaru ce ta fitar da Najeriya a bugun fanariti da hakan ta sa Najeriya ba ta halarcbi gasar wasannin Olamfik bangaren kwallon kafa na mata ba da ya gudana a Ingila. Yanzu ma ba za ta halarci wanda zai gudana a Brazil ba kenan.
Eukatorial Guinea dai ta fitar da Najeriya da ci 3-1 idan kuma aka hada sakamakon gida da waje ya zama 3-2 kenan. Najeriya ta doke Ekuatorial Guinea a gida ne da ci 1-0 kimanin makwanni biyu da suka wuce sai ga shi a wasa zagaye na biyu ta kasa kai bantenta.