El Classico: Barcelona ta yi wa Real Madrid zazzaga har gida

Barcelona ta zazzaga wa Madrid ƙwallo huɗu a raga a gaban magoya bayanta.

El Classico: Barcelona ta yi wa Real Madrid zazzaga har gida

Ƙungiyar ƙwallon kafa ta Barcelona ta yi wa Real Madrid dakan sakwara da ƙwallaye huɗu rigis a filin wasa na Santiago Bernabeu.

Ƙungiyoyi sun kara da juna a gasar Laliga a mako na 11.

Ɗan wasan gaban Barcelona, Robert Lewandowski ne ya fara jefa ƙwallo a minti na 54, bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

Kazalika, ɗan wasan ya sake jega ƙwallo a minti na 56. Lamine Yamal ya jefa ƙwallo a minti na 77, sai Rapinha ya ƙara ƙwallo ta huɗu a minti na 84.

Barcelona na ci gaba da jan ragamar gasar da maki 30, yayin da Madrid ke biye mata da maki 26.

Barcelona ta buga wasanni 11, ta yi nasara a guda 10 tare da yin rashin nasara a wasa ɗaya.

Real Madrid da ke mataki na biyu a teburin gasar ta buga wasanni 11, ta yi nasara a guda bakwai, sai kunnen doki a wasanni uku tare da rashin nasara a hannun Barcelona.

Lewandowski ne ya fi kowa yawan jefa ƙwallaye a raga, inda yake da ƙwallo 14, sai Mbappe na Real Madrid da ke bi masa baya da ƙwallo shida.