El-Kanemi ta lashe Kofin Shugaban Kasa karon farko cikin shekaru 32

Kungiyar El-Kanemi Warriors ta kuma samu kyautar naira miliyan 50 a dalilin lashe gasar da ta yi.

El-Kanemi ta lashe Kofin Shugaban Kasa karon farko cikin shekaru 32

Shugaban Hukumar Kwallon Kafa na Kasa (NFF), Ibrahim Gusau da Ministan Wasanni, John Enoh suna mika wa kyaftin din El-Kanemi Warriors kofin da kungiyar ta lashe.

Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Jihar Borno, El-Kanemi Warriors ta lashe gasar cin kofin shugaban kasa (President Federation Cup) ta maza ta shekarar 2024, wanda ya zama nasararta karon farko cikin shekaru 32.

Wannan na zuwa ne bayan El-Kanemi Warriors ta doke Abia Warriors da ci 2-0 a wasan karshe da suka fafata ranar Asabar a filin wasa na Mobolaji Johnson da ke Jihar Legas.

Dan wasan El-Kanemi Warriors, Nasiru Salihu, wanda aka bayyana a matsayin mafi bajinta a gasar, shi ne ya jefa kwallon farko da ta biyu da suka bai wa kungiyarsa nasara a wasan da aka kece raini.

Tun farkon fara wasan ne dai El-Kanemi ta samu damar bugun da daga kai sai mai tsaron raga, amma Salihu ya barar.

Amma daga bisani ya fanshi kansa, inda ya zura kwallo ta farko a minti na 32 da fara wasa, kuma haka aka karkare har zuwa tafiya hutun rabin lokaci.

Bayan an dawo ne Salihu ya kara kwallo ta biyu a minti na 68, lamarin da ya tabbatar wa kungiyarsa da nasarar da ta samu da ta kai ta ga lashe wannan gasa.

Mataimakin Gwamnan Jihar Borno, Umar Usman Kadafur wanda yana cikin mahalarta kallon wasan, ya nuna matukar farin cikinsa ga nasarar da kungiyar ta samu.

El-Kanemi, wadda koci Ali Zubairu ya jagoranta, ta samu wannan nasarar ce da ta ba ta damar lashe kofin shugaban kasa karo na uku jimilla a tarihin kungiyar.

Aminiya ta ruwaito cewa, kungiyar wadda ta lashe wannan gasa shekaru 32 da suka gabata ta kuma samu kyautar naira miliyan 50 a dalilin lashe gasar da ta yi a wannan karon.

Shugaban Hukumar Kwallon Kafa na Kasa (NFF), Ibrahim Gusau da Ministan Wasanni, John Enoh ne suka mika wa kyaftin din El-Kanemi Warriors kofin da kungiyar ta lashe.

Nasarar da El-Kanemi ta samu a gasar cin kofin shugaban kasa ta kuma tabbatar da samun gurbi a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta CAF na kakar wasa mai zuwa wadda za ta wakilci Nijeriya.

Wannan nasarar dai na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar ta samu karin girma a Gasar Firimiyar Nijeriya NPFL a kwanakin baya, wanda hakan ya kara wa kungiyar kwarin gwiwar nasarorin da ta samu a bana.

An sace ɗan shekara 79 a Kaduna

Gwamnatin Borno ta ayyana Litinin a matsayin hutu

Shugabannin ECOWAS na ganawa a Abuja

Gwamnati za ta yanka wa hakimai albashi a Sakkwato