ICPC ta hana El-Rufai ganin likita —Hadiminsa
Da an ga idon El-Rufai, za a gani a fili cewa idon babu lafiya, sakamakon kumbura da kuma ja da ya yi, amma duk da haka, hukumar ta ƙi bari ya ga likitan da ya dace domin samun lafiya
Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, yana fama da matsanancin ciwon ido a yayin da yake tsare a hannun hukumar ICPC.
Mai ba El-Rufai shawara kan harkokin watsa labarai, Muyiwa Adekeye, ne ya sanar da haka, a yayin da tsohon gwamnan ya shafe sama da kwanaki 100 a tsare a hannun hukumar ICPC, wadda take sere da El-Rufai tun a watan Fabrairu, inda take tuhumar sa da almundahanar wasu kuɗaɗen gwamnatin jihar lokacin da yake gwamna.
Muyiwa Adekeye ya sanar da haka ne ciki wani saƙon koke ya fitar inda ya zargi hukumar ICPC da tauye haƙƙin El-Rufai na ganin likita duk da umarnin kotu da aka gabatar wa hukumar.
Ya bayyana cewa duk da cewa da an ga idon El-Rufai, za a gani a fili cewa idon babu lafiya, sakamakon kumbura da kuma ja da ya yi, amma duk da haka, hukumar ta ƙi bari ya ga likitan da ya dace domin samun lafiya.
- Hanyoyin zuwa Katsina sun zama tarkon mutuwa
- Alhazan Jigawa sun angwance bayan kammala aikin Hajjin bana
Adeleke ya ƙara da cewa da fakro an kai El-Rufai asibiti a ranar Alhamis, amma ciwon ya ƙara ta’azzar daga baya, kuma jami’an hukumar sun hana a kai shi asibiti ko a kawo likita ya duba shi domin samun lafiya.