El-Rufai ne ke yaki da Atiku ta Hukumar NPA- Abdullahi Sugar

Wani na kusa da tsohon mataimakin shugaban qasa, Alhaji Atiku Abubakar,  Alhaji Muhammadu Abdullahi Sugar ya ce abin da ke faruwa da kamfanin Atiku mai suna Intels ba zai rasa nasaba da sa hannun gwamnan Jihar Kaduna ba. Alhaji Muhammadu Sugar ya yi wannan bayanin ne a lokacin da yake jawabi a kan dakatar da […]

El-Rufai ne ke yaki da Atiku ta Hukumar NPA- Abdullahi Sugar

Wani na kusa da tsohon mataimakin shugaban qasa, Alhaji Atiku Abubakar,  Alhaji Muhammadu Abdullahi Sugar ya ce abin da ke faruwa da kamfanin Atiku mai suna Intels ba zai rasa nasaba da sa hannun gwamnan Jihar Kaduna ba.

Alhaji Muhammadu Sugar ya yi wannan bayanin ne a lokacin da yake jawabi a kan dakatar da yarjejeniyar da Hukamar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa (NPA) ta shiga da Kamafanin Intels, inda ya ce wannan wata bita-da-qullin siyasa ce kawai El-Rufai ya shirya ta hannun shugabar Hukumar Hadiza Bala Usman.

A cewar Sugar “Mun san cewa akwai sa hannun El-Rufai; Amma muna so ya san cewa ko mai gidanshi Olusegun Obasanjo ya ja da Atiku ya bar shi.

“Duk qoqarin da ya yi domin vata mishi suna a wancan lokaci bai haifar da xa mai ido ba,” inji Sugar.

Hakanan kuma, Alhaji Abdullahi ya qara da cewa “Atiku ya taimaka matuqa wajen fafutukar neman zaven shugaban qasa Muhammadu Buhari, amma bayan an samu nasara, ba a ba shi dama ya kawo na kusa da shi ba, ya yi shiru bai ce uffan ba. Amma kuma sai a saka masa da irin wannan hukuncin. Gaskiya wannan lamarin abin takaici ne,” inji Abdullahi Sugar.

Sannan daga qarshe ya yi kira ga Majalisar Tarayya da ta dubi wannan xanyen hukunci da Hukumar NPA ta yanke, domin a cewarshi kamfanin Intels ba ta karya wata qa’ida ba.