El-Rufai ya aike wa Ribadu takarda kan zargin shigo da guba mai hatsari cikin Najeriya 

Tsohon gwamnan na Kaduna ya bayyana damuwarsa kan yadda ofishin ke amfani da ikonsa wajen kama ‘yan adawa.

El-Rufai ya aike wa Ribadu takarda kan zargin shigo da guba mai hatsari cikin Najeriya 

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya buƙaci Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkar Tsaro, Nuhu Ribadu, ya yi bayani kan rahotannin da ke cewa ofishinsa ya shigo da “thallium sulphate”, wani sinadari mai hatsarin gaske.

A cikin wasiƙar, El-Rufai ya ce yana neman ƙarin haske a matsayinsa na ɗan ƙasa, inda ya tambayi manufar shigo da sinadarin, adadin da aka shigo da shi, wanda aka sayar, da kuma matakan tsaro da aka ɗauka.

Ya rubuta cewa: “Ina rubuta wannan wasiƙa ne a matsayin ɗan ƙasa wanda ya damu domin neman ƙarin bayani kan bayanan da suka nuna cewa an sayo kusan kilo 10 na sinadarin Thallium Sulphate ta Ofishin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkar Tsaro…

“Tunda wannan sinadari na da matuƙar hatsari ana taƙaita amfani da shi, yana da muhimmanci a tabbatar da waɗannan bayanai.”

Ya ƙara da cewa manufarsa ita ce tabbatar da bin doka, tsaro, da kuma gaskiya domin ƙara amincewar jama’a.

Batun ya biyo bayan zargin da El-Rufai ya yi cewa Ribadu ya bayar da umarnin kama shi a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, yayin wata hira da ya yi da gidan talabijin na ARISE.

Ya ce wani mutum ya saurari wayar da Ribadu ya yi da kuma shirin da yake yi na kama shi, wanda hakan ne ya sa mutumin ya sanar da shi.

“Gwamnati na ganin ita kaɗai ta ke sauraron kiran waya, amma mu ma muna da hanyoyinmu… Wani ya saurari wayarsa ya faɗa mana cewa shi ne ya bayar da umarnin.”

El-Rufai, yana zargin jam’iyya mai mulki na farautarsa saboda siyasa.