El-Rufai ya bai wa Sarki Sanusi II mukami
Kwana daya da tube Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II daga gadon sarauta, Gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-Rufai, ya ba shi mukami a Hukumar Fadada Zuba Jari ta Kaduna (KADIPA), inda ya zama mataimakin Hukumar. A cikin wata sanarwa da aka fitar daga gidan gwamnatin jihar Sir Kashim Ibrahim, wanda mai taimakawa Gwamnan kan watsa […]
Gwamna El Rufai da Malam Muhammadu Sanusi II
Kwana daya da tube Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II daga gadon sarauta, Gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-Rufai, ya ba shi mukami a Hukumar Fadada Zuba Jari ta Kaduna (KADIPA), inda ya zama mataimakin Hukumar.
A cikin wata sanarwa da aka fitar daga gidan gwamnatin jihar Sir Kashim Ibrahim, wanda mai taimakawa Gwamnan kan watsa labarai ya rattaba hannu, mai suna Muyiwa Adekeye. A cikin sanarwar na bayyana cewa, mukamin da aka bai wa tsohon Sarkin nada alaka ne da kokarinsa wajen inganta tattalin arziki da kawo ci gaba a fannoni da dama a fadin duniya.
Sanarwar ta kara da cewa, wannan mukamin da aka bai wa Sanusi II a Hukumar KADIPA, Mataimakiyar Gwamnan jihar ce zata jagoranci masu gudanarwar Hukumar sai kuma wasu manyan jami’an gwamnatin jihar.