El-Rufa’i ya fara rusau a Sabuwar Kaduna

Gwamnatin Jihar Kaduna a karkashin Gwamna Nasir El-Rufa’i ta fara rusa gidajen da aka gina a kan filiyen gwamnati a Sabuwar Kaduna.Idan ba a manta ba gwamnatin jihar ta sha alwashin kwato filayen gwamnati, musamman filayen makarantu da asibitoci da aka yi gine-gine a kai ba bisa ka’ida ba.A ’yan watannin baya gwanmnatin ta rusa […]

El-Rufa’i ya fara rusau a Sabuwar Kaduna
El-Rufa’i ya fara rusau a Sabuwar Kaduna

Gwamnatin Jihar Kaduna a karkashin Gwamna Nasir El-Rufa’i ta fara rusa gidajen da aka gina a kan filiyen gwamnati a Sabuwar Kaduna.
Idan ba a manta ba gwamnatin jihar ta sha alwashin kwato filayen gwamnati, musamman filayen makarantu da asibitoci da aka yi gine-gine a kai ba bisa ka’ida ba.
A ’yan watannin baya gwanmnatin ta rusa gidaje da shaguna da ke cikin makarantun Alhudahuda, Zariya da shagunan da ke jingine da makarantar firamare ta Titin Maiduguri a cikin garin Kaduna. Sai dai ta dakatar da rusa gidajen bayan wani umarni da kotu ta bayar na a jingine hakan zuwa lokacin da za ta saurari wata kara da aka kai mata.
A ranar Talatar da ta gabata ce Hukumar Bunkasa Biranen Kaduna (KASUPDA) ta yi wa Unguwar danbushiya da ke Sabuwar Kaduna dirar mikiya ta rika rusa gidajen.
Hukumar KASUPDA wadda ta samu rikiyar jami’ain tsaro a cikin motoci kirar Hilud bakwai cikin shirin ko-ta-kwana, ta hadu da turjiya daga mazauna yankin danbushiya inda sai da jami’an tsaro suka rika harbi a sama domin tarwatsa matasan da suka fito domin nuna bacin ransu a kan matakin.