El-Rufa’i ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2018
Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i ya gabatar da daftarin kasafin kudin shekarar 2018 ga al’ummar jihar. Da yake jawabi a taron al’ummar jihar, El-Rufa’i ya yi kira ga jama’ar jihar su kawo shawarar ayyukan da suke son gwamnatin jihar ta yi musu. Ya ce gwamnati ta tsara kasafin kudin shekarar 2016 da shekarar 2017 […]

Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i ya gabatar da daftarin kasafin kudin shekarar 2018 ga al’ummar jihar.
Da yake jawabi a taron al’ummar jihar, El-Rufa’i ya yi kira ga jama’ar jihar su kawo shawarar ayyukan da suke son gwamnatin jihar ta yi musu.
Ya ce gwamnati ta tsara kasafin kudin shekarar 2016 da shekarar 2017 bayan da jama’ar jihar suka kawo shawarwarin ayyukan da gwamnatin ba ta sanya cikin kasafin kudin ba.
Gwamnan ya bayyana cewa taron al’ummar jihar an shirya shi ne don gwamnati ta saurari ra’ayoyin jama’a tare da basu damar damawa da su a gwamnati.