El-Rufai ya kai wa Obasanjo ziyara
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ziyarci tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a Abeokuta, jihar Ogun a ranar Lahadi.
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ziyarci tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a Abeokuta, jihar Ogun a ranar Lahadi.
El-Rufai ya bayyana cewa ya ziyarci tsohon ubangidansa ne tare da abokansa, kimanin mako guda bayan da Sarkin Ijebu, Oba Sikiru Adetona ya nada El-Rufai a matsayin Gbobaniyi na kasar Ijebu.
Tsohon gwamnan ya ce “yau (Lahadi) na ziyarci maigidana, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, tare da abokaina a gidansa na Abeokuta,” amma bai bayyana dalilin ziyarar ba.
A watan Satumba, El-Rufai ya bayyana Obasanjo a matsayin wanda ya fi kowa samun nasara ta fuskar bunkasar tattalin arziki, samar da ayyukan yi, da hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya.
- Ban gayyaci Tinubu don yin sulhu a rikicin Ribas ba —Wike
- Yadda Emefiele ya mallaki bankuna 3 ta barauniyar hanya
ya bayyana haka ne a wani zama da aka yi a yayin taron Africa In the World a Afrika ta Kudu.
El-Rufai ya yi aiki a matsayin Darakta-Janar na Hukumar Kula da Kamfanonin Gwamnati (BPE) da kuma Ministan Babban Birnin Tarayya a gwamnatin Obasanjo na shekaru takwas.