El-Rufa’i ya nada Sakataren Gwamnatin Jihar Kaduna

Sabon Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rura’i ya nada wasu manyan mukarraban gwamnatinsa a shekaranjiya Laraba. Wata sanarwa da El-Rufa’i ya sanya wa hannu da kansa ta bayyana Malam Balarabe Abbas Lawal a matsayin Sakataren Gwamnatin Jihar.Sanarawar ta kara da cewa an nada Malam Salisu Suleiman a matsayin Babban Sakataren Gwamnan (PPS), sai Mista Abu […]

El-Rufa’i ya nada Sakataren Gwamnatin Jihar Kaduna
El-Rufa’i ya nada Sakataren Gwamnatin Jihar Kaduna

Sabon Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rura’i ya nada wasu manyan mukarraban gwamnatinsa a shekaranjiya Laraba.

Wata sanarwa da El-Rufa’i ya sanya wa hannu da kansa ta bayyana Malam Balarabe Abbas Lawal a matsayin Sakataren Gwamnatin Jihar.
Sanarawar ta kara da cewa an nada Malam Salisu Suleiman a matsayin Babban Sakataren Gwamnan (PPS), sai Mista Abu Musa Sheyin a matsayin Sakataren Mataimakin Gwamna Mista Barnabas Yusuf Bala.
Gwamnan ya kuma bayyana nada Bala Yunusa a matsayin Mataimakin Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnati (bangaren Harkokin Majalisa) da kuma Mista Samuel Aruwan a matsayin Maitaimaka masa kan harkokin watsa labarai. Kuma sanarwar ta ce nade-naden za su fara aiki ne daga yau Juma’a.
Malam Lawal, wanda tsohon malamin jami’a ne ya taba zama shugaban ma’aikata na Gwamnan a lokacin da yake Ministan Birnin Tarayya.
Sannan darakta ne a kwamitin yakin neman zaben Nasir El-Rufa’i kuma shi ne shugaban kwamitin karbar mulki na Jam’iyyar APC a Jihar Kaduna.
A wani labarin kuma Shugaban Majalisar Wakilai ta Tarayya Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya sauka daga kujerarsa kujerarsa shugabancin majalisar gabanin karewar wa’adinsa a farkon watan gobe.
Alhaji Aminu Tambuwal ya dauki wannan mataki ne domin samun damar daukar ranstuwa a matsayin sabon Gwamnan jiharsa ta Sakkwato da ake sa ran yi a yau Juma’a.
Aminu Tambuwal ya sauka daga kujerar tasa ce a yayin wani zaman na ban-kwana da majalisar ta yi a shekaranjiya Laraba.