El-Rufai ya nemi afuwa ko mu maka shi a kotu — Gidauniyar Ɗahiru Bauchi
Gidauniyar ta ce idan bai nemi afuwarsu ba za su maka shi a kotu.

Gidauniyar Sheikh Ɗahiru Bauchi ta buƙaci Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, da ya nemi afuwar ɗaliban malamin bisa abin da ta kira rashin adalci da aka musu.
Idan kuwa bai yi hakan ba kafin ƙarshen watan Ramadan, za su maka shi a kotu.
- An sanya dokar hana fita bayan kashe sabuwar amarya a Jigawa
- HOTUNA: NDLEA ta kama hodar iblis da aka ɓoye a cikin carbi da takalma
Wannan na ƙunshe ne a wata takarda da gidauniyar ta fitar, wadda Sayyadi Aliyu Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi ya sanya wa hannu.
A cewar takardar, dole ne El-Rufai ya fito ya yarda da laifinsa sannan ya nemi afuwar gidauniyar, ɗalibanta da jagoranta, Sheikh Ɗahiru Bauchi.
Gidauniyar ta zargi tsohon gwamnan da bayar da umarni ga jami’an tsaro don su kai samame a makarantun tsangayar Sheikh Ɗahiru Bauchi, inda aka kama wasu ɗaliban karatun Alƙur’ani har zuwa gidansa.
Har yanzu, akwai ɗaliban da ba a san inda suke ba.
Sayyadi ya bayyana cewa an yi hakan ne da gangan domin a tozarta Sheikh Ɗahiru Bauchi da kuma hana ci gaban ilimin addini da ya ke yi.
Ya ce idan har El-Rufai bai nemi afuwa ba kafin ƙarshen Ramadan, za su kai ƙararsa ga Shugaban Ƙasa, ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam, da kotu.
Idan kuwa duka ba su yi musu adalci ba, za su mika ƙarar ga Allah ta hanyar addu’a.