El-Rufai ya sa hannu kan dokar dandake masu fyade
Duk wanda aka kama mace ko na miji da yin fyade to za a yi masa dandaka
Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya rattaba hannu a kan sabuwar dokar Penal Code da ta tanadi yin dandaka ga maza da mata da suka aikata fyade a jihar.
A ranar Laraba da dare gwamnan ya sanar ce ya sanya hannu a kan dokar da majalisar ta yi wa gyaran fuska, wanda yanzu ya zama dokar Penal Code 2020.
A makon jiya ne Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta amince da gyaran fuskar da ta yi wa Doka ta biyar ta Penal Code (2017) ta jihar, wanda Gwamna El-Rufai ya gabtar mata, yana bukatar kara tsaurar bangaren dokar da ta ce “Duk wanda aka kama da aikata fyade to za a yanke masa hukuncin daurin rai-da-rai”.
Sauye-sauyen da sabuwar tokar ta tanadar su ne:
“Dun wanda aka kama da laifin yi wa yaro dan kasa a shekara 14 fyade to za a dandake shi a kuma kashe shi.
“Duk wanda ya yi jima’i da yaro dan kasa da shekara 14 to za a yanke masa hukuncin dandakewa da kuma kisa.
“Idan aka kama mace da laifin yi wa yaro fyade to kotu za ta yanke mata hukuncin dandaka ta hanyar bilateral salpingectomy sannan a kashe ta.
“Idan wanda aka yi wa fyaden ya haura shekara 14, to za a yi wa mai fyaden dandaka da daurin rai-da-rai.
“Idan wanda ya yi fyaden karamin yaro ne, to kotu za ta ba da umarnin a sanya sunasa a rajistar masu manyan laifuka sannan Antoni Janar ya wallafa a kafafen yada labarai.
“Idan shari’ar fyaden ta shafi yara ‘yan kasa da shekara 14 ne, to wajibi ne a bukaci rahoton asibiti”.