El-Rufai Ya Sake Ganawa Da Jiga-Jigan Jam’iyyar SDP A Abuja
Wannan zama shi ne kusan na uku a kasa da kwana goma tun da El-Rufai ya fara bayyana a wani taro mai kama da siyasa.
Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna ya sake ganawa da waɗansu jiga-jigan jam’iyyar SDP a gidan Sanata Abubakar Gada tare da shugaban jam’iyyar na kasa Shehu Musa Gabam.
Wannan zama dai shi ne kusan na uku a kasa da kwana goma tun da El-Rufai ya fara bayyana a wani taro mai kama da siyasa.
Ziyarar ta El-Rufai ta fara yamutsa hazo a fagen siyasa wadda wasu ke ganin tana nuna ina ya dosa a Zaben 2027 da ke tafe ne.
El-Rufai ɗaya ne daga cikin waɗanda suka tsaya kai da fata sai Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya mulki kasar nan.
Sai dai wani abin mamaki El-Rufain bai samu sahalewar Majalisar Dattawan Najeriya domin zama minista a gwamnatin da ya ba da gagarumar gudunmawa wurin kafawa ba.
- Ba Zan Bai Wa Wani Ɗana Shawarar Zama Soja Ba — Matar Laftanar Kanar Ali
- Yadda Gwamnatin Kaduna Ta Kasa Miƙa Ɗaliban Kuriga Da Aka Ceto Ga Iyayensu
Yayin wannan taro, an ga Sanata Teslim Folarin, na jam’iyyar APC daga Jihar Oyo, da Sanata Nazif Suleiman, wani jigo a jam’iyyar PDP daga Jihar Bauchi.
A makon da ya gabata dai El-Rufai ya shirya wani shan ruwa inda aka ga mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu da Kashim Ibrahim-Imam (wani jigo a jam’iyyar APC), Shehu Musa Gabam shugaban jam’iyyar SPD na kasa, da waɗansu manyan ’yan siyasa.
Mai taimakawa Malam Nasiru a bangaren kafafen sadarwa Muyiwa Adekeye ya ce wannan taro ne kawai na sada zumunta wanda kowa na iya shiryawa.
Ya ce “tsabagen siyasar da ke zuciyar mutane ne ya sa ake yi wa ziyarce-ziyarcen fassarar siyasa, amma wannan ba wani abu ba ne, zumunci ne kawai.”
Muyiwa Adekeye ya yi wannan martani ne ga waɗanda ke cewa El-Rufai na shirin tsayawa takara ne a karkashin jam’iyyar SPD a zaben 2027.
Waɗansu hotunan ganawar El-Rufai da jiga-jigan jam’iyyar SDP