El-Rufai ya sassauta dokar hana fita a Kaduna

Gwamnatin Jihar Kaduna ta sassauta dokar hana fita a fadin jihar, inda a yanzu ta koma daga karfe 6:00 na safe zuwa karfe 6:00 na yamma, domin bai wa al’umma damar ci gaba da gudanar da al’amuransu kamar yadda aka saba. Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar, Samuel Aruwan ya yi karin bayani […]

El-Rufai ya sassauta dokar hana fita a Kaduna

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai

Gwamnatin Jihar Kaduna ta sassauta dokar hana fita a fadin jihar, inda a yanzu ta koma daga karfe 6:00 na safe zuwa karfe 6:00 na yamma, domin bai wa al’umma damar ci gaba da gudanar da al’amuransu kamar yadda aka saba.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar, Samuel Aruwan ya yi karin bayani game da sassauta dokar a ranar Laraba, inda ya bayyana cewa bayan zaman da gwamnati ta yi da jami’an tsaro a kan yanayin tsaro a jihar, hakan ya basu damar sassauta dokar a fadin jihar baki daya.

Aruwan ya ce “Daga ranar Alhamis, 29 ga watan Oktoban 2020, mutanen jihar na da damar ci gaba da gudanar da al’amuransu kamar yadda suka saba daga karfe 6:00 na safe zuwa karfe 6:00 na yamma.”

“An hana gudanar da zirga-zirga da daddare a yayin da dokar za ta fara aiki daga karfe 6:00 na yamma zuwa karfe 6:00 na safe,” a cewar Aruwan.

Sanarwa ta ce, ana kira da jama’ar jihar Kaduna da su bi umarnin doka, su kuma sanya ido da kai rahoton duk wani abu da basu gamsu da shi ba, yayin da kuma aka bukaci su bawa dukkan hukumomin tsaro hadin kai domin sauke nauyin da rataya a wuyansu.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa