El-Rufai ya sauya dokar kullen coronavirus
Gwamnatin jihar Kaduna ta kara tsawaita wa’adin dokar kullen hana yaduwar cutar coronavirus tare da fitar da sabbin matakai. Mataimakiyar Gwamnan jihar Hadiza Balarabe Sabuwa ta ce sabbin matakan sassauta dokar dakile cutar za suu ba jama’a karin damar yin harkokinsu. Hadiza ta ce gwamna Nasir El-Rufai ya ce a makon nan ma za a […]
Gwamnatin jihar Kaduna ta kara tsawaita wa’adin dokar kullen hana yaduwar cutar coronavirus tare da fitar da sabbin matakai.
Mataimakiyar Gwamnan jihar Hadiza Balarabe Sabuwa ta ce sabbin matakan sassauta dokar dakile cutar za suu ba jama’a karin damar yin harkokinsu.
Hadiza ta ce gwamna Nasir El-Rufai ya ce a makon nan ma za a bude jihar a ranakun Laraba da Alhamis. Amma daga ranar Litinin 1 ga watan Yuni kuma, sassaucin zai koma ranakun Talata da Laraba da Alhamis.
Kasuwannin wucin gadi za su bude daga karfe 10 na safe zuwa 4 na yamma a duk ranakun sassaucin.
Saukin zai ba da damar bude karin bangarorin gwamnati da ba wa masu sana’o’i damar su yin harkokinsu cikin bin matakan dakile cutar COVID-19.
Saukin zai ba da damar bude karin bangarorin gwamnati da ba wa masu sana’o’i damar su yin harkokinsu cikin bin matakan dakile cutar COVID-19
Ta ce a makonni biyu masu zuwa kuma ma’aikatun gwamnatin jihar za su tsara komawarsu aiki cikin kiyaye ka’idojin dakile yaduwar cutar.
Za a ci gaba da rufe makarantu da wuraren ibada da kasuwanni, amma an yi wa gidajen abinci sassaucin sayar da abincin da za a tafi da shi kadai.
Wuraren motsa jiki da wuraren shakatawa da otal-otal ma za su ci gaba da kasancewa a rufe.
Sai dai sanarwar ta ce gwamnatin jihar za ta tuntubi masu ruwa da tsaki a fannonin addini da sufuri da kasuwanni da makarantu kan yadda za a bude bangarorin ba tare da wani hadari ba.
Sanarwar ta kuma yaba wa ‘yan jihar bisa juriya da hadin kai da suka bayar a lokacin dokar hana fitar.
Ta ce yawancin wadanda ke dauke da cutar a jihar na da tarihin tafiye-tafiye zuwa wasu jihoji.