El-Rufai ya so a kai Film Village Kaduna, amma… —Sani Mu’azu
Naira biliyan hudu aka ware don aikin a kasafin Gwamnatin Tarayya domin gina katafaren dandalin Film Village a Kano
Wani jigo a harkar fina-finan Hausa ta Kanywood, Alhaji Sani Mu’azu, ya ce Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ya so a kai aikin katafaren dandalin shirya finafinai, wato Film Village, wanda aka hana ginawa a Jihar Kano zuwa jiharsa.
A wata zantawa da ya yi da Aminiya a Jos, Sani Mu’azu ya ce sai dai kuma da yake kudin aikin a kasafin kudi yake, shekarar har ta kare ba a yi amfani da shi ba, don haka aka mayar baitul malin gwamnati.
- Kotu Ta Ci Sheikh Abduljabbar Tarar Naira Miliyan 10
- Za Mu Tabbatar An Bi Wa Ummita Hakkinta —Ganduje
A cewarsa, a lokacin Naira biliyan hudu aka ware don aikin a kasafin Gwamnatin Tarayya.
“[Hana aikin] ba karamar illa ba ce ga tattalin arzikin Jihar Kano da Arewa baki daya da masana’antar Kanywood,” inji shi.
Ya kara da cewa, “A lokacin mun fito, mun yi babatu kan a fahimci cewa wannan waje da za a yi ba waje ne na badala ba.
“Masana’anta ce za a kafa, kuma idan da an bari an kafa ta an sanya kayan aiki, da an rage rashin aikin yi ga matasan Jihar Kano, da an sami cigaba sosai a masana’antar Kanywood, amma aka kasa fahimtar haka.”
Alhaji Sani Mu’azu ya bayyana cewa yana cikin wadanda suka nuna jin dadinsu da kokarin da Honarabul Abdulmuminu Jibrin ya yi, na samo kudi masu yawa haka don aikin.
Ya ce ganin irin kudaden da aka ware da kuma kokarin da aka yi a kawo abin Kano, sai gwamnonin jihohin Kudu suka taso suna neman a kai musu aikin.
“Amma dai mu ba mu hakura ba, muna kokarin fadakar da ’yan siyasarmu wadanda suke sauraron mu, kan cewa Film Village alheri ne ba ga harkar fim kadai ba, al’ummar da ta samu aka gina Film Village a cikinta ma za ta amfana sosai.
“Idan ka dubi masu aikin sufuri, wato direbobi da masu motoci za su samu aikin yi.
“Masu harkar abinci, har masu wanki da guga da manoma za su samu dama, don Film Village waje ne da kusan komai za a iya fitowa da shi.
“Za a gina gari, za a gina fada. Idan za a yi wannan aiki, kowa zai samu aikin da zai yi.
“Teloli da masu kwado da linzami da masu aikin fata da magina, duk za su samu aiki.
“Mutane, musamman manya malamanmu da ’yan siyasarmu su fahimci alherin kawo wannan Film Village.
“Mu dubi manya-manyan biranen duniya, kamar New York da London da sauransu – akwai manya-manyan Film Village a wadannan birane.
“Mu dubi irin yadda suka taimaka wa wadannan birane wajen bunkasa tattalin arziki.”
Za ku iya karanta cikakkiyar tattaunawar nan ba da jimawa ba a jaridar Aminiya da kuma aminiya.dailytrust.com.