EL-Rufai ya zabi Hadiza Balarabe mataimakiya
Gwamnan jihar Kaduna Nasir Ahmad El-Rufai ya sanar da zaben Dakta Hadiza Balarabe a matsayin matar da za ta zame masa mataimakiya a zaben 2019. Zaben Hadiza dai ya sha suka a wurin wasu ‘yan jihar, musamman ‘yan yankin Kudancin Kaduna wadanda ke ganin bai kamata Gwamna El-Rufai ya zabi musulmi ba tun da a […]
Gwamnan jihar Kaduna Nasir Ahmad El-Rufai ya sanar da zaben Dakta Hadiza Balarabe a matsayin matar da za ta zame masa mataimakiya a zaben 2019.
Zaben Hadiza dai ya sha suka a wurin wasu ‘yan jihar, musamman ‘yan yankin Kudancin Kaduna wadanda ke ganin bai kamata Gwamna El-Rufai ya zabi musulmi ba tun da a al’adance Kirista ake zaba domin su tafi tare a matsayin maitaimaka masa.
Wasu ‘yan jihar sun yaba wa gwamna El-Rufai bisa yin la’akari da kwarewa ba siyasa ba a zaben mataimakiyar tasa.