El-Rufa’i ya zabi kwamishinoni 13
Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufaii, ya zabi mutum 13 don zama kwamshinoni a gwamnatinsa. Wata wasika da ya aike ga Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Alhaji Aminu Shagali, Gwamna El-Rufa’i ya bukaci ’yan majalisar su duba tare da amincewa da wandada ya zaba inda ya hada da sunan ma’aikatun da zai tura kowannensu domin ba […]
Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufaii, ya zabi mutum 13 don zama kwamshinoni a gwamnatinsa.
Wata wasika da ya aike ga Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Alhaji Aminu Shagali, Gwamna El-Rufa’i ya bukaci ’yan majalisar su duba tare da amincewa da wandada ya zaba inda ya hada da sunan ma’aikatun da zai tura kowannensu domin ba majalisar damar tantace su bisa gaskiya da adalci.
Wadanda ya zaba sun hada da, Farfesa Jonathan Andrew Nok, Kiwon Lafiya da Hajiya Rabi M.G. Abdulsalam, Harkokin Mata da Inganta Rayuwa da Injiniya Suleiman Aliyu Lere, Albarkatun Ruwa da Muhammed Sani Abdullahi, Kasafi da Tsare-Tsare da Dokta Manzo Daniel Maigari, Aikin Gona da Gadun Daji da Muhammad Bashir Sa’idu, kananan Hukumomi da Harkokin Masarautu.
Sauran su ne, Suleiman Abdu Kwari, Kudi da Dokta Shehu Usman Adamu, Ilimi da Kimiyya da kere-kere da Dokta Ya’u Usman Idris, Muhalli da Albarkatun kasa da Daniel Auta, Matasa da Wasanni da Al’adu da Shehu Balarabe, Kasuwanci da Masana’antu da Yawon Shakatawa da Amina Ruth Dyeris-Sijuwade, Shari’a da kuma Usman Mahmud Hassan, Ayyuka, Gidaje da Sufuri.