El-Rufai zai gina ‘Film Village’ a Kaduna
Gwamnatin Kaduna da masu ruwa da tsaki sun rabbata hannu kan yarjejeniyar kafa alkaryar fina-finai (Film Village).
Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanar da amincewarta da kafa alkaryar fina-finai da aka fi sani da Film Village.
Tuni gwamnatin ta sanya hannu a kan takardar yarjejeniyar gina cubiyar.
- An yi garkurwa da hafsan dan sanda a Kwara
- Batar Naira Tiriliyan 5: Majalisa ta soma binciken hukumomin 252
- NAJERIYA A YAU: Yadda Za Ku Tabbata ’Yan Siyasa Na Cika Alkawurran Zabe
An sanya hannun ne a taron bunkasa kasuwanci da tattalin arziki na jihar wato Kaduna Economic and Investment Summit da ake ci gaba da yi a jihar.
Kwamishina kuma Magajin Garin Kaduna, Malam Muhammad Hafiz Bayero, ne ya sanya hannun tare da sauran masu ruwa da tsaki.
A sanarwar da Gwamnatin Jihar Kaduna ta fitar, ta ce alkaryar fina-finan za ta taimaka wajen bunkasa harkokin fina-finai.
A cewar sanarwar, alkaryar za ta samar da ayyuka ga jarumai da marubuta da masu kwalliya da sauran masu aikin bayan fage a fina-finai.
Idan ba a manta ba, a shekarun baya ne aka amince da gina alkaryar a Jihar Kano, amma wasu mutanen suka nuna rashin amincewarsu, wanda hakan ya sa dole gwamnatin jihar din ta bar batun.