El-Rufai zai rushe kamfanoni 9 mallakar Makarfi
Gwamnatin jihar ta aike wa Makarfi takardun shaidar kwace mallakar kamfanonin tara.
Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna, ya soke lasisin mallakar kamfanoni tara na tsohon gwamnan jihar, Sanata Ahmed Muhammed Makarfi.
An kuma shirya rushe kamfanoni tara mallakar tsohon gwamnan Jihar.
- NNPP ba ta kudin kalubalantar nasarar Tinubu a kotu —Buba Galadima
- Karbo bashin $800m zalunci ne —Sani Brothers ga Buhari
Aminiya ta fahimci cewa an kai sanarwar janye hakkin mallaka ga jami’an kamfanonin da abin ya shafa.
Sanarwar ta fito ne daga Daraktan kamfanin rake da ke lamba 11 a Murtala Square, Alhaji Ibrahim Makarfi wanda ya mayar da martani da cewa, “lauyoyinmu za su mayar da martani kan kwace hakkin mallakar kamfanonin”.
Sai dai da yake mayar da martani kan soke hakkin mallakar a wani sakon da ya aike wa Sanata Makarfi, ya tabbatar da samun wasikun soke kamfanonin har guda tara.
Ya ce, “Akwai babban batu. Muna bukatar ganawa da Ustaz Yunus (SAN) domin mu garzaya kotu don dakatar da gwamnatin jiha; kawai sun aiko mana da takardun soke mallaka guda tara”.
Daga cikin kadarorin da abin ya shafa sun hada da filaye guda biyar a Mogadishu, filaye uku a kan titin Kwato, da fili daya a Doka.
A cikin takardun soke hakkin mallakar da magatakardar hukumar kula da bayanan kasa ta Kaduna (KADGIS) ya sanya wa hannu, Mahmud Aminu ya ce, “An umarce ni da na sanar da ku cewa mai girma Gwamnan Jihar Kaduna a cikin ikon da aka ba shi a karkashin sashe na 28 (5) (a) da (b) na dokar amfani da filaye ta 1978, ya kwace hakkin mallakar wadannan kadarori da aka ambata”.