El-Rufa’i zai sauya fasalin masarautun Kaduna
Wani bincike da Aminiya ta gudanar ya gano cewa Gwamnan jihar Kaduna, Nasiru el-Rufa’i ya kafa kwamiti don ya sake fasalin masarautu 32 a jihar. Aminiya ta gano cewa kimanin masarautu 13 wadanda mafiyawancinsu ke yankunan tsakiya da kuma kudancin jihar za a sake musu suna. A watan Yuni ne gwamnatin jihar ta kori […]

Wani bincike da Aminiya ta gudanar ya gano cewa Gwamnan jihar Kaduna, Nasiru el-Rufa’i ya kafa kwamiti don ya sake fasalin masarautu 32 a jihar.
Aminiya ta gano cewa kimanin masarautu 13 wadanda mafiyawancinsu ke yankunan tsakiya da kuma kudancin jihar za a sake musu suna.
A watan Yuni ne gwamnatin jihar ta kori hakimai 313 da masu unguwanni dubu hudu da 453 a yunkurin da gwamnatin take yi na rage kudin da kananan hukumomin jihar ke kashewa.
Sakamakon haka jihar ta koma mai hakimai 77 da kuma masu unguwanni dubu daya da 4,29 da suke a da kafin shekarar 2001.
Wadansu daga cikin hakiman da lamarin ya shafa tuni suka kalubalanci matakin gwamnatin jihar a kotu.