El-Rufai: EFCC ta tsare shi, ICPC da DSS na jiran sa

A yayin da EFCC ke ci gaba da tsare shi Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) da kuma DSS da kotu suna jiran fitowarsa domin amsa wasu tambayoyi

El-Rufai: EFCC ta tsare shi, ICPC da DSS na jiran sa

El-Rufai ya kwana a hannun Hukumar EFCC a yayin da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) da Hukumar DSS da kotu suke jiran ya zo gaban kowannensu domin amsa wasu tambayoyi kan wasu zarge-zarge na daban.

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya kwana a tsare a hannun Hukumar Yaƙi da masu Ƙarya Tattalin Arzikin Ƙasa (EFCC) inda yake amsa tambayoyi kan zargin almundahana da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci.

Daga cikin abubuwan da EFCC take bincikar tsohon gwamnan, har da zargin almundahanar Naira biliyan 432 a zamanin mulkinsa daga shekarar 2015 zuwa 2023 a Jihar Kaduna.

A yayin da EFCC ke ci gaba da tsare shi bayan ya gabatar da kansa a safiyar ranar Litinin, a yau  Talata Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) tana jiran zuwansa ofishinta domin amsa wasu tambayoyin na daban, kamar yadda ya yi mata alƙawari.

Kazalika Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) tana jiran sa domin bincikar da game da zargin naɗar wayar Mashawarcin Shugaban Ƙasa kan Sha’anin Tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribaɗu, wanda Ofishinsa (ONSA) ya bayyana a matsayin barazana ga tsaron ƙasa.

A ranar Litinin kuma, Gwamnatin Tarayya ta hannun Hukumar DSS ta maka El-Rufai a gaban kotu kan zargin manyan laifuka uku, bayan ya yi zargin cewa Ofishin NSA ya shigo da sinadarin Thallium Sulphate mai kisa.

Ofishin ya ƙaryata zargin na El-Rufai tare da cewa zai gudanar da bincike kan lamarin wanda ke da matuƙar muhimmanci.

Mutuwa Adeleke, kakakin El-Rufai ya sanar bayan mai gidan nasa ya shafe awanni a EFCC cewa, “El-Rufai ya amsa gayyatar EFCC bisa raɗin kansa kuma sun yi tattaunawa mai ma’ana ba tare da nuƙu-nuƙu ba, kuma jami’an sun nuna ƙwarewa. Har yanzu yana tare da su. Har yanzu yana tare da su,” in ji shi a cikin wani saƙo da ya wallafa a X a cikin dare.