ElBaradei ya yi murabus daga mataimakin Shugaban Masar
Mataimakin Shugaban kasa na riko, Mohammed Elbaradei ya yi murabus daga mukaminsa, saboda mummunan farmakin da jami’an tsaro suka kai a sansanin magoya bayan hambararren shugaban kasa Mohammad Mursi. Elbaradei ya nuna rashin gamsuwarsa kan matakin da gwamnatin kasar ta dauka kan masu adawa da ita, kamar yadda yake kunshe a takardar ajiye aiki da […]
Mataimakin Shugaban kasa na riko, Mohammed Elbaradei ya yi murabus daga mukaminsa, saboda mummunan farmakin da jami’an tsaro suka kai a sansanin magoya bayan hambararren shugaban kasa Mohammad Mursi.
Elbaradei ya nuna rashin gamsuwarsa kan matakin da gwamnatin kasar ta dauka kan masu adawa da ita, kamar yadda yake kunshe a takardar ajiye aiki da ya rubuta ga shugaban riko, Adly Mansour.
A takardar ajiye aikinsa da ya aike wa Shugaban riko, Adly Mansour, ElBaradei ya ce, “Wadanda suka ci gajiyar wannan tashin hankalin, su ne masu kiran a yi tashin hankali da ta’addanci da sauran gungun masu tsattsauran ra’ayi.”
“Sanin ku ne cewa, na san hanyoyin lallama da suka kamata a bi don shawo kan karon batta a tsakanin al’umma, an gabatar da tsare-tsaren warware matsaloli da aka gamsu da su har mu samu daidaito a daukacin kasa baki dayua,” kamar yadda ya rubuta a wasikarsa.
“Wannan al’amari yana da matukar wahala a gareni in ci gaba da daukar nauyin matakin da ban amince da shi ba , kuma ina cike da tsoron sakamakon da matakin zai haifar,” inji shi.